A cewar rundunar sojin Rasha, jiragen yakin sun kammala aikin da aka tura su yi a Syria.
Babban hafsan sojin Rasha Valery Gerasimov ne ya sanar da matakin janye makaman sojin a Syria kamar yadda babban kwamandan sojin kasar kuma shugaban kasa Vladimir Putin ya bukata.
Taimakon sojin Rasha da suka shiga Syria a watan satumban 2015, ya taimakawa dakarun Assad yakar ‘yan tawaye tare da kawato birnin Aleppo.
Jiragen dai sun kai farmaki 420 tare da kai hare hare a waurare 1,252 na maboyar ‘yan twayen Syria cikin watanni biyu.
Sai dai kuma, har yanzu Rasha tace tana da sauran karfin soji a Syria
Masu sharhi dai na ganin fara ficewar makaman yakin na Rasha zai taimakawa kokarin sulhun da kasar ke yi tsakaninta da ‘yan tawayen bisa jagorancin Turkiya, Iran da ita kanta Rasha na kawo karshen rikicin kasar ta Syria.288